Wata kotun Majistare da ke Kaduna ta bayar da umarnin tsare wani matashi dan shekara 27 mai suna Musa Haruna a gidan gyaran hali, bisa zarginsa da yunkurin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 9 fyade.
Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, wanda bai amsa rokon Haruna ba na rashin hurumin sauraron karar ya umarci ‘yan sanda da su mayar da fayil din karar zuwa ga daraktan kararrakin jama’a na jihar Kaduna domin samun shawarar lauya.
Sai dai ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Satumba.
Ana tuhumar Haruna da ke zaune a Ungwan Rimi Kaduna da yunkurin fyade.
Mai gabatar da kara, Insp. Chidi Leo, ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Satumba a gidansa.
Leo ya ce wanda ake tuhumar ya yaudari yarinyar mai shekaru 9 a cikin dakinsa kuma ya yi yunkurin yi mata fyade.
Mai gabatar da kara ya kara da cewa kukan yarinyar ya sanar da wasu makwabta da suka kubutar da ita tare da mika wanda ake tuhuma ga ‘yan sanda.
Laifin a cewarsa ya sabawa tanadin sashe na 207 na dokar jihar Kaduna ta shekarar 2017 (kamar yadda aka gyara).