Wata kotun majistare da ke zamanta a yankin Ota a jihar Ogun ta umarci wata mata mai suna, Biola Joshua, mai shekaru 43 da ta share harabar makarantar sakandare ta Iju-Ebiye na tsawon watanni shida.
Rundunar ‘yan sandan ta tuhumi Miss. Joshua da laifin hada baki, cin zarafi da kuma rashin zaman lafiya, bayan ta kutsa kai cikin makarantar da danta ke karatu da ‘yan daba.
Mai shigar da kara na ‘yan sanda, Cynthia Ejezie, ta ce, Joshua, da danta da sauran su, a ranar 11 ga Maris, 2021, da misalin karfe 2:00 na rana, sun mamaye ofishin shugaban makarantar da na jami’in lafiya na makarantar, ya kuma yi musu rauni a jiki.
A hukuncin da ta yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a Shotunde Shotayo ya yankewa matar hukuncin tare da umarce ta da rika share makarantar daga karfe 8:00 na safe zuwa 11:00 na safe kowace rana na tsawon watanni shida.
Alkalin kotun ya ba da umarnin cewa, makarantar ta bude littafi ga mai laifin, inda za a rika rubuta ayyukanta na yau da kullum.
Shotayo, ya ba ta zabin biyan tarar Naira dubu 30,000.