Kotun ƙoli ta tabbatar da Caleb Mutfwang a matsayin halastaccen gwamnan jihar Filato.
Mutfwang na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 525,299 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda da ya samu ƙuri’u 481,370 a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a Jos, babban birnin jihar ya tabbatar da zaɓen gwamna Mutfwang.
Sai dai kotun ɗaukaka ƙara a Abuja a nata hukuncin ranar 19 ga watan Nuwamban bara ta soke nasarar Mr Mutfwang lamarin da ya sa gwamnan ya garzaya kotu domin ɗaukaka ƙara da nufin ƙalubalantar hukuncin ƙaramar kotun.