fidelitybank

Kotu ta tabbatar da Tambuwal da Wamako

Date:

Wata kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja a ranar Talata, ta tabbatar da zaben tsofaffin gwamnonin jihar Sokoto biyu, Aminu Tambuwal da Aliyu Wamakko a matsayin sanatoci masu wakiltar Sokoto ta Kudu da Sokoto ta Arewa.

Zaben Tambuwal wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar kuma dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kalubalantar tsohon Sanata mai wakiltar gundumar, Ibrahim Danbaba yayin da Wamakko ya kalubalanci tsohon mataimakin gwamnan jihar, Manir Dan’ iya iya.

Alkalan mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Mustapha Muhammad a cikin shari’o’i guda biyu, sun yi fatali da karar da Danbaba ya shigar a kan Tambuwal tare da bayar da tarar Naira 500,000 ga wadanda ake kara da kuma jam’iyyarsa ta siyasa ta PDP.

Da yake jawabi, daya daga cikin manyan lauyoyin wanda ake kara kuma na PDP, Suleiman Usman, ya ce yayin da aka amince da zaben Tambuwal, karar da tsohon mataimakinsa ya kai wa Wamakko ya ci tura.

Usman ya ce, “Kotu ta yanke hukuncin ne kan zaben Sanata guda biyu a jihar.

“Yayin da kotu ta tabbatar da zaben Sanata Tambuwal, masu shari’a uku a cikin hikimar su kuma sun ci tarar N500,000 ga wanda ya shigar da kara domin goyon bayan wanda ake kara da kuma PDP.

“A halin da ake ciki, kotun kuma bisa hikimarta ta yi watsi da karar da muka shigar a madadin tsohon mataimakin gwamna, Manir Dan’iya a kan tsohon gwamna kuma Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Arewa, Aliyu Wamakko.

“Kotu ta kuma ci tarar wanda ba zan iya tunawa ba a kan wanda muke karewa a kan wanda ake kara a wannan shari’ar.”

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp