fidelitybank

Kotu ta tabbatar da takarar Sanata Adamu Aliero

Date:

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin ɗan takarar kujerar sanata ta Kebbi ta tsakiya a ƙarkashin inuwar jam’iyyar PDP.

A ranar Litinin ne tawagar alƙalan kotun biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a China Centus Nweze, suka yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da na babbar kotun tarayya suka yanke a baya, a kan zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar.

Alƙalan sun yanke hukuncin cewa ƙalubalantar ayyana Saidu Haruna a matsayin ɗan takarar sanata a jam’iyyar PDP yana kan daidai.

Haka kuma kotun ƙolin ta tabbatar da zaɓen Dakta Abubakar Yahaya Abdullahi a matsayin ɗan takarar sanatan Kebbi ta arewa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

A yanzu Sanata Aliero – wanda tsohon gwamnan jihar Kebbi ne – zai fafata da gwamnan jihar mai ci Atiku Bagudu, wanda ke takarar kujerar sanatan a jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

the nation newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp