Kotun Ƙolin ta tabbatar wa Gwamnan Ebonyi Dave Umahi, takararsa ta kujerar sanata da yake yi a babban zaɓen 2023 mai zuwa.
Cikin wani matakin bai-ɗaya da suka yanke, rukunin alƙali biyar na kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Ekekere-Ekun sun kori ƙarar da mai adawa da takarar tasa Princess Ann Agom-Eze ta shigar a ranar Juma’a.
Kafofin labarai a Najeriya sun ruwaito cewa alƙalan sun amince cewa ƙarar ba ta cancanci a saurare ta ba kuma dalilin da ya sa suka kore ta kenan.
Agom-Eze ta kai ƙarar ce da zimmar kotun ƙolin ta jingine hukunce-hukuncen da Babbar Kotun Tarayya da Kotun Ɗaukaka Ƙara suka yi na amincewa da sakamakon zaɓen da ya ayyana Umahi a matsayin wanda ya yi nasara.
Ita ce ta zo ta biyu a zaɓen da aka gudanar lokacin da aka bayyana Austin Umahi a matsayin wanda ya yi nasara, wanda ɗan uwa ne ga Gwamna Dave Umahi.
Sai dai gwamnan ya shiga takarar ce bayan kayen da ya sha a zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin ƙasa, inda ƙaninsa Austin ya janye tare da ba shi tikitin takarar.
Hakan na nufin wannan ne hukunci na ƙarshe da za a yi a shari’ar.