Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta kasa da ta jihar ta yanke kan zaben Majalisar Wakilai ta Kano na mazabar Kumbotso.
Hukuncin farko ya bayyana Mannir Babba Danagudi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben yayin da ya cire Idris Kawu na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin zababben wakilin mazabar Kumbotso a majalisar wakilai ta tarayya.
Alkalan kotun uku karkashin jagorancin Mai shari’a Tunji Oyebamuji ne suka yanke hukunci, inda suka bayyana cewa karamar kotun ta tafka kura-kurai ta hanyar ba da fifiko kan hukuncin da aka yanke kan takardar shaidar Idris Kawu, duk da rashin gabatar da ita ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Kotun daukaka kara ta kuma ce karamar kotun ta yi kuskure ne ta hanyar dogaro da shaidun da aka sa a gaba domin yanke hukunci.
Bugu da kari, kotun ta tabbatar da cewa Mannir Babba Danagudi ya kasa bayar da sahihin shedu da za su tabbatar da soke nasarar da Idris Dankawu ya samu a zaben mazabar tarayya ta Kumbotso.