fidelitybank

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamnan Sokoto

Date:

Kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan a jihar Sokoto, ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Ahmad Aliyu.

Kotun ta kori karar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Saidu Umar ya shigar, inda yake kalubalantar sakamakon zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta yi watsi da karar ne saboda rashin gamsassun hujjoji.

Mai magana da yawun gwamnan jihar a Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce sun yi farin ciki da hukuncin kotun.

“Mun godewa Allah da jam’iyyarmu da al’ummar jihar Sokoto domin zaɓar ɗan takarar mu da suka,” in ji Bawa.

Ya bayyana cewa ‘yan jam’iyyar PDP na da damar Ɗaukaka ƙara idan har ba su gamsu da hukuncin ba.

Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP a jihar ta Sokoto, Hassan Sahabi, ya bayyana wa BBC cewa hukuncin ya zo mu su da ba-zata kasancewar suna da gamsassun hujjoji da suka shigar a gaban kotu.

”Akwai batun maguɗin zabe da kuma aringizon kuri’u da aka yi, akwai bayanan da muka gabatar waɗanda da an tsaya an yi nazari akan su yadda ya kamata, to da muna kyautata zaton za a yi mana adalci”.

Jam’iyyar ta PDP ta kuma nuna rashin gamsuwa da yadda aka yi watsi da karar da suka shigar game da bambancin suna da aka suke zargi a takardun ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Ahmad Aliyu.

Sahabi ya ce za su tattauna da lauyoyinsu domin ɗaukar mataki na gaba.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp