Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Nasir Idris a matsayin zababben gwamnan jihar Kebbi da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Kotun a wani hukunci da ta yanke a yammacin ranar Juma’a ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Janar Aminu Bande suka shigar a gabanta saboda rashin cancantar su.
A wani hukunci na bai daya da mai shari’a Ndukwe Anyanwu ya yanke, kotun daukaka kara ta warware dukkan wasu batutuwa biyar da aka tsara domin tabbatar da gaskiya ga gwamnan da kuma jam’iyyar PDP.
Mai shari’a Anyanwu ya bayyana cewa ba a kafa tuhume-tuhume na jabun shedu da aka kai wa mataimakin gwamnan jihar, Abubakar Umar Tafida ba kamar yadda doka ta tanada.
Ta kuma kara da cewa batutuwan rashin bin tanadin dokar zabe wajen gudanar da zaben ba za su iya tsayawa ba saboda masu shigar da kara sun kasa tabbatar da yadda zarge-zargen ya shafi zaben.
Daga bisani mai shari’a Anyanwu ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kebbi wadda a baya ta yi watsi da karar da PDP ta shigar tare da tabbatar da zaben gwamnan.