Kotun sauraren kararrakin zabe da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis, ta tabbatar da zaben gwamna Nasir Idris a matsayin zababben gwamnan jihar Kebbi.
Kotun da ke karkashin mai shari’a Ofem I. Ofem ta yanke hukuncin ne a ranar Alhamis.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana Idris na jam’iyyar All Progressives Congress, APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Amma Janar Aminu Bande (mai ritaya) na jam’iyyar PDP ya shigar da kara mai shafuka 722 yana kalubalantar zaben gwamna Idris a zaben da aka gudanar ranar 18 ga Maris.