fidelitybank

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Legas

Date:

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Legas ta tabbatar da zaben gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Kotun ta yi watsi da karar da aka shigar kan zaben Sanwo-Olu a wani hukunci da ta yanke ranar Litinin.

A wani hukunci da illahirin alkalan suka amince da shi, kuma Mai shari’a Mikail Abdullahi ya karanta a madadin alkalan uku ranar Litinin, kotun ta yanke hukuncin cewa korafin jam’iyyar PDP da dan takarar Olajide Adediran ba shi da tushe, don haka kuma sun yi watsi da karar.

A kokarin tabbatar da hukuncin da ta yanke, kotun da farko nanata kin amincewar farko-farko da bangarorin da ke cikin shari’ar suka nuna kafin ta yi nazari game da batutuwan da ta bijiro da su don yin shari’a.

Kotun ta saurari bahasi a kan tambayar ko tana da hurumin sauraron karar, Mai shari’a Mika’il Abdullahi ya ce tabbas kotun tana da hurumi.

Sai kuma batu na biyu da ke neman hukunci a kan ko jam’iyyar APC ta ba da sunan Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat bisa hanyar da ta dace su tsaya mata takara a zaben 18 ga watan Maris.

Kotun ta kafa hujjoji da tanade-tanaden tsarin mulki da kuma na kundin zabe da dumbin shari’o’in da aka yanke hukunci dangane da batun, inda ta jaddada cewa korafin batu ne da ya kamata a ce tuni an kammala da shi kafin gudanar da zabe kuma ba shi da alaka da zabukan da aka kalubalanta.

Kotun ta kuma ce masu korafin ba ‘ya’yan jam’iyyar APC ba ne wadda ake kara ta hudu don haka ba su da hurumin kalubalantar zaben fid-da-gwanin da ya fito da ‘yan takarar biyu.

legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp