Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori, ya sake samun nasara a kotun koli tare da yin watsi da karar da jam’iyyar Social Democratic Party, SDP da dan takararta na gwamna Kenneth Gbagi suka shigar kan rashin cancantar su.
A wani hukunci na bai daya da ta yanke a ranar Juma’a, kotun kolin ta yi watsi da duk wasu dalilai da zarge-zargen da aka yi kan zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris din shekarar da ta gabata.
Mai shari’a Mohammed Garba Lawal, wanda ya yanke hukuncin, ya ce zargin da ake yi na cewa jam’iyyar PDP, dan takararta, Oborevwori, bai cancanci zaben ba abin dariya ne domin babu wata shaida da ta tabbatar da zargin.
Mai shari’a Lawal ya yi watsi da ikirarin cewa zaben bai inganta ba, kuma ba a yi zaben gwamna da mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.
A wani hukunci a cikin daukaka karar da jam’iyyar Labour Party, LP, da dan takararta na gwamna, Ken Pela, Kotun Koli ta yi watsi da karar saboda rashin gaskiya da rashin cancanta.
Mai shari’a Musa Uwani Aba-Aji, wanda ya yanke hukuncin, ya ce karar ba ta da wani amfani domin wadanda suka shigar da karar ba za su iya tabbatar da ko daya daga cikin zarge-zargen nasu ba.
Daga bisani mai shari’a Aba-Aji ya yi watsi da karar gaba dayanta.
A halin da ake ciki dai, dukkan koke-koke guda uku da jam’iyyun APC, SDP da LP suka shigar, an yi watsi da su ne saboda rashin cancanta.


