Kotun ƙoli da ke zaman ta a Abuja ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad na PDP ya samu a zaɓen gwamna na shekarar 2023.
A hukuncin da ta zartar a yau Juma’a, kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Siddique Abubakar wanda ya ƙalubalanci hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da na sauraron ƙorafin zaɓen jihar, waɗanda suka tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed.
Wannan dai shi ne mataki na ƙarshe a shari’ar da ake yi ta tantance ingancin nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen na watan Maris.
Bala Mohammed ya lashe zaɓen ne a ƙoƙarin sa na neman karo na biyu na mulkin da ya fara a a watan Mayun 2019.
Tun da farko, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Bauchi da kotun ɗaukaka ƙara duk sun kori ƙararsa, suna cewa ba ta da tushe.
Saddique Abubakar dai yana tunƙahon cewa takardun zaɓe masu yawa da aka yi amfani da su, ba a cike su yadda ya kamata ba. Sannan ya yi zargin cewa ba a yi biyayya ga kundin dokokin zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri’ar zaɓen gwamna a Bauchi ba.
Sai dai, kotun ɗaukaka ƙara ta ce ɗan takarar na APC ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu da za su tallafi zarge-zargensa.
Duk da haka, bai yi ƙasa a gwiwa ba, a Juma’ar nan Saddique Abubakar yana fatan kotun ƙoli za ta yi hujjojin da ya gabatar duban basira, kuma ta ba shi gaskiya, yayin da abokin takararsa na PDP ke fatan alƙalan kotun kamar takwarorinsu na kotunan baya, su kori wannan ƙara.