A ranar Juma’a ne kotun koli ta tabbatar da zaben Francis Nwifuru a matsayin gwamnan jihar Ebonyi.
Mai shari’a Tijjani Abubakar wanda ya yanke hukuncin, ya yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Chukwuma Odii suka shigar.
Mai shari’a Abubakar ya bayyana karar a matsayin rashin cancanta
Kotun daukaka kara da ke Legas ta tabbatar da zaben Nwifuru a matsayin zababben gwamnan jihar Ebonyi.
A wani mataki na bai daya, kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Jummai Sankey ya yi watsi da karar da Chukwuma Odii na PDP ya shigar.
Kwamitin ya kuma warware duk wasu batutuwa guda biyar da aka gabatar a kan wanda ya shigar da kara tare da yin watsi da daukaka karar saboda rashin cancanta.
Mai shari’a Sankey ya ce jam’iyyar PDP da ‘yan takararta ba su da hurumin shiga cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar APC dangane da batun tantance ‘yan takara.
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Ebonyi da ke zamanta a Abuja ita ma ta amince da zaben Nwifuru a matsayin gwamna.
INEC ta bayyana Nwifuru na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.
Nwifuru ya samu kuri’u 199,131 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Ifeanyi Odii na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 80,191.
Bernard Odoh, ya zo na uku da kuri’u 52,189.
Odoh da jam’iyyarsa ta All Progressives Grand Alliance, APGA, sun kalubalanci ayyana Nwifuru a matsayin zababben gwamnan jihar inda suka bukaci kotun da ta soke zabensa bisa dalilan da ake zarginsa da yin satifiket na jabu da kuma rashin cancantar tsayawa takarar zaben.
Dan takarar na APGA ya bayyana cewa Nwifuru, a lokacin zaben, har yanzu dan jam’iyyar PDP ne, don haka jam’iyyar APC bai cancanci daukar nauyin zaben ba.
Odoh ya ci gaba da cewa Nwifuru bai cancanci tsayawa takara ba saboda ya mika takardar shaidar karya ga INEC.
Ya bukaci kotun da ta bayar da umarnin gudanar da zabe karo na biyu tsakanin sauran ‘yan takara biyu da suka samu kuri’u mafi yawa a zaben da ya gabata tare da cire gwamnan daga shiga cikinsa.