fidelitybank

Kotu ta tabbatar da kujerar gwamnan Binuwai

Date:

Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar Benue da ke zamanta a Makurdi, ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Hyacinth Alia na jam’iyyar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta yi watsi da karar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Titus Uba, ya shigar gabanta, inda yake kalubalantar sakamakon zaɓen.

Kotun ta ce ta kori ƙarar ne saboda ba ta da hurumin sauraron batun da aka kai mata.

Tawagar alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Karaye, sun bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar ne saboda abin da aka kai mata ya shafi batutuwa ne na gabanin zaɓe kamar yadda yake a sashe na 285 na dokar zaɓe.

Mista Titus na zargin Mista Alia da gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta jabu a lokacin da ya tsaya takara.

Sai dai kotun ta ce a gaban hukumar zaɓe ta INEC ya kamata ya kai ƙorafinsa.

Sakamakon zaɓen da INEC ta fitar a wancan lokaci, ya nuna cewa Mista Alia ya samu nasara ne da kuri’u 473,933, inda ya doke takwaransa na PDP, Titus Uba, wanda ya samu kuri’u 223,913

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp