Kotun koli ta tabbatar da zaɓen Agbu Kefas na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Taraba.
Kotun kolin a wani mataki na bai daya ta yi watsi da daukaka karar da Farfesa Yahaya Sani na jam’iyyar NNPP ya yi kan rashin cancantar Kefas tsayawa takarar gwamnan jihar.