Kotun daukaka kara da ke zamanta a Legas ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da APC da ‘yan takarar gwamnan su suka shigar kan zaben gwamna Alex Otti na jihar Abia.
A wani mataki na bai daya da suka yanke ranar Asabar, kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara sun tabbatar da nasarar Otti a rumfunan zabe, inda suka ce ya yi daidai da tanadin dokar zabe.
Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa kararrakin da masu daukaka karar suka kawo ba su da inganci, domin sun kasance kamar “wasan wasan barkwanci da aka kawo a tsarin dimokradiyya”.
Kotun ta ce batutuwan zama ‘yan jam’iyyar siyasa lamari ne kafin zabe, wanda kuma ya rataya a wuyan jam’iyyar.
Ta kuma ce tun lokacin da Otti ya koma jam’iyyar Labour, ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar ya kuma mika sunansa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya cancanci tsayawa takara.
Dangane da batun Bimodial Voter Accreditation System, BVAS, da jam’iyyar PDP da dan takararta suka kawo, kotun daukaka kara ta ce wadanda suka shigar da kara sun kasa nuna ko kuma alakanta takardun shaidarsu da wasu sassan shari’ar.
Hukuncin ya haifar da murna a tsakanin magoya bayan Gwamna Otti a wasu sassan jihar.


