Kotun koli ta yi watsi da ɗaukaka karar da Tonye Cole, ɗan jam’iyyar APC ya shigar in da yake ƙalubalantar nasarar Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP a Zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023 a jihar Rivers.
Kotun ta tabbatar da Fubara a matsayin gwamnan jihar.
Kotun ta ce Cole bai tabbatar da zarginsa ba na cewa Fubara bai cancanta tsayawa takarar ba saboda bai bai yi murabus daga mukamin babban akanta janar na jihar Rivers ba kafin zaɓen wanda hakan ya saɓawa dokar zaɓe.
Kotun ta ce karar da aka shigar bai yi nasara ba kuma ta yi watsi da shi.