Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta tabbatar da nasarar Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da APC da ‘yar takararta Aishatu Ahmed Binani suka shigar gabanta suna ƙalubalantar nasarar Fintiri.
Alƙalan kotun sun ce kotu ta yi watsi da ƙarar ne saboda lauyoyin masu shigar da ƙara sun kasa gamsar da kotun da hujjoji.
Tun da farko hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar cikin watan MAris a matsayin wanda bai kammala ba, inda aka ƙarasa zaɓen cikin watan Afrilu.
Inda INEC ɗin ta ayyana Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.