Kotun ƙoli ta tabbatar da Dauda Lawan Dare, a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP qa jihar Zamfara.
Hukuncin kotun na zuwa ne kawana hudu kafin zaɓen gwamnonin jihohin ƙasar da za a gudanar ranar 11 ga watan Maris.
A hukuncin da suke yanke alƙalan kotun biyar ƙarƙashin jagoranci alƙalan mai shari’a Adamu Jauro, duka sun amince da yin watsi da ɗaukaka ƙarar da Dakta Ibrahim Gusau ya shigar gabanta yana ƙalubalantar takarar dauda.
Kotun ta ce ta amince da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ke Sokoto ta yi ranar 6 ga watan Janairun da muke ciki, wanda ya amince da zaɓen fitar da gwani na biyu da aka yi wanda a shi ne Dauda Lawan ya yi nasara.
A zaɓen Dauda Lawan ya samu nasara da ƙuri’a 442 a kan abokan takarar tasa.