Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Zamfara ta ki amincewa da bukatar wani bangare mai goyon bayan shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Gwamna Bala Mohammed na gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC).
Kungiyar ta garzaya kotu domin ta ba da umarnin gudanar da taron na NEC yayin da rikicin bangaran jam’iyyar ya kara ruruwa.
Da yake yanke hukunci kan karar, Mai shari’a Salim Ibrahim ya ki amincewa da bukatar.
Wani bangare na jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin gwamnan Bauchi Bala Mohammed, sun tunkari kotu suna neman a ba su umarnin gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC).
A baya dai wasu gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Mohammed sun yi yunkurin tsige shugaban riko na kasa Amb. Umar Damagum.
Matakin ya kara dagula rikicin cikin jam’iyyar, yayin da wasu masu ruwa da tsaki musamman masu biyayya ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike suka nuna adawa da matakin.
Ita ma babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin hana jam’iyyar cire Damagum.
An shigar da karar bangaren Mohammed ne a babbar kotun tarayya da ke jihar Zamfara.