Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha da ke zamanta a Yenagoa a ranar Juma’a, ta soke zaben Fred Agbedi na jam’iyyar PDP na mazabar tarayya ta Sagbama/Ekeremor na jihar Bayelsa.
Kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gaggauta janye takardar shaidar da ta baiwa Agbedi tare da gudanar da sabon zabe na masu kada kuri’a 20,000 a mazabar da aka hana su shiga zaben ba bisa ka’ida ba.
Michael Olomu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne ya garzaya kotun, inda ya bukaci a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben saboda tashe-tashen hankula da suka dabaibaye tsarin zaben.
Ya yi zargin cewa tashe-tashen hankula da ake zargin abokin hamayyarsa ne ya kitsa su, ya yi tasiri matuka wajen sahihancin zaben.
Olomu ya ce zaben bai gudana a unguwanni biyar ba, amma an tattara sakamako a Unguwannin da abin ya shafa sun hada da Ward 5 a Ebedebiri, Ward 11 a Ofoni, Sagbama, da Ward 12 a Ekeremo, tare da Ward 3 da 4 a Ofoni, Sagbama.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Agbedi ya bayyana shirinsa na shiga zaben da za a kara.


