Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal, a ranar Talata, ta soke zaben ‘yan majalisar wakilai hudu na jam’iyyar Labour a jihar Ribas.
Alkalin kotun, Mai shari’a Turaki Mohammed, a hukuncin da ya yanke, ya amince da jam’iyyar PDP, cewa jam’iyyar Labour ba ta bi dokar zabe ba a yayin gudanar da zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar dokokin jihar guda hudu.
Mai shari’a Mohammed ya kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta fitar da sunayen ‘yan takarar jam’iyyar Labour da abin ya shafa da suka hada da na Obio/Akpor 1 da 2 da Tai da kuma jihar Gokana.
Sai dai alkalin kotun bai amince da jam’iyyar PDP ba cewa zaben fidda gwani na jam’iyyar Labour da ta fitar da ‘yan takarar Ahoada Gabas da Yamma ba hukumar INEC ta sa ido ba.
A halin da ake ciki, lauyan ‘yan takarar jam’iyyar Labour, Uche Olewunne ya sha alwashin cewa wadanda yake karewa za su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.