fidelitybank

Kotu ta sauke tuhuma 8 da gwamnati ke yi wa Nnamdi Kanu

Date:

Alƙaliyar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke tuhuma takwas daga cikin 15 da gwamnatin tarayya ke tuhumar madugun ‘yan aware na kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Tuhume-tuhumen takwas na cikin laifukan da aka kara kan tuhume-tuhumen da ake yi wa shugaban ‘yan awaren.

Yayin da take watsi da karar, Mai Shari’a Binta Nyako ta ce, zarge-zargen ba su bayyana laifin da wanda ake karar ya aikata ba.

Mai shari’ar ta ce, sato shugaban IPOB din da aka yi da manufar gudanar da bincike abu ne halastacce.

Ta kuma ce, da ma akwai umarnin kamu a kan Kanu bayan tserewa daga kasar a gaban kotu.

Sai dai lauyoyin da ke kare shi sun dage kan cewa, gwamnatin Najeriya ta karya dokar ƙasa da ƙasa tare da take hakkin Kanu, da sato shi daga wata ƙasar a bara.

Duk da cewa, har yanzu hukumomi ba su bayyana inda da kuma yadda aka kama Mista Kanu, kuma aka ta so ƙeyarsa ba, dangi da kuma lauyoyinsa na cewa, an kama shi ne a ƙasar Kenya cikin wani yanayi mai sarƙaƙiya.

Gwamnatin Kenya dai ta musanta wannan zargi. An ki ba da belin shugaban kungiyar ta IPOB a zaman na yau.

Ana zarginsa ne da ayukkan ta’addanci da kuma cin amanar ƙasa kuma yana fuskantar ɗaurin rai-da-rai idan aka same shi da laifi.

www.leadership ng.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp