Sashen Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta soke nasarar da Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Simon Mwadkwon ya samu a zaben Sanatan Filato ta Arewa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.
Hakan ya kasance kamar yadda kotun daukaka kara ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 90.
Kotun ta yanke hukuncin ne kan karar da Chris Giwa na jam’iyyar APC da Gyang Zi na jam’iyyar Labour Party (LP) suka shigar.
Giwa da Zi sun daukaka kara kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta kasa/jihar da ke Jos, jihar Filato ta yanke, wadda tun farko ta tabbatar da Mwadkwon na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben sanata.
Sun ce Mwadkwon bai cancanci tsayawa takara ba saboda PDP ba ta da tsari.
Da yake karanta hukuncin kotun, Mai shari’a E. Daudu, ya ce PDP ta gaza cika umarnin babbar kotu saboda kananan hukumomi 12 ba su halarci taron na jam’iyyar ba.
“Kotu ta yi cikakken bincike game da batun da aka fi mayar da hankali.
“Don gujewa rikici, na yarda da masu kara cewa dole ne kotu ta kare umarnin wata kotu.
“Na yarda da wanda ya shigar da kara cewa wanda ake kara na uku ba shi da wani tsari mai inganci kuma ba zai iya da’awar cewa ya gabatar da wanda ake kara na biyu (Mwadkwon) a zaben ba.
“Saboda sakamakon binciken da wannan kotun ta samu, daukaka kara, ya yi nasara saboda ba a bi umarnin kotu ba.
“An umurci wanda ake kara na farko da ya sake gudanar da zaben Sanata a Filato ta Arewa cikin kwanaki 90,” in ji Daudu.