fidelitybank

Kotu ta sassauta wa Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda wajen belin sa

Date:

Kotun Majistare ta jihar Kano mai lamba 58 karkashin jagorancin Aminu Gabari a ranar Alhamis ta yi nazari kan sharuddan belin da ta ayyana a baya kan Abdulmajid Sani Kwamanda.
Kadaura24 ta rawaito cewa, sakamakon rokon da lauyan Abdulmajid Danbilki kwamanda Barista Tajuddeen Funsho ya yi a gaban kotun.
Da yake gabatar da rokon, Barista. Funsho ya bukaci kotun da ta sake duba sharuddan da ta gindaya a baya a kan wanda yake karewa, inda ya ce wanda ake kara zai ci gaba da zuwa kotu, domin sauraren laifukan da ake kararsa akan su waÉ—anda suka shafi bata sunan gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
A martanin da ya mayar, lauyan masu shigar da kara, Barista. Wada Ahmad Wada, ya ce, batun sake duba belin, kotu ce ta yanke hukunci, inda ya yi fatan za a bi ka’idojin shari’a da adalci wajen sake nazarin.
A hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun ya umurci Danbilki da ya gabatar da mutane 2 wadanda suka hada da: mahaifinsa ko wakilinsa, maimakon Wakilin Gabas na masarautar Kano da aka bukata tun da fari.
Hakazalika, kotun ta umurci wanda ake kara da ya gabatar da limamin na duk wani masallaci da ke unguwar Koki, ko kuma limamin kowane masallacin da ya ke gudanar da sallarsa a wajen.
Mai Shari’a Gabari ya kuma ba da umarnin cewa, haka nan wanda ake tuhuma zai iya kiran duk wani shugaban addini a cikin al’umma, idan har bai samu wani Imami da zai tsaya masa ba.
Wannan ya maye gurbin Babban Limamin Masallacin Hajiya Mariya Sanusi Dantata da ke unguwar koki da kotun ta ambata a baya.
Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga Afrilu, 2023, domin ci gaba da ambato.

latest nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp