Kotun Amurka ta samu dan shugaban kasar Joe Biden, wato Hunter Biden, da laifin aikata manyan laifuka guda uku.
Zargin ya samo asali ne daga wani abin da ya faru a watan Oktoban 2018, lokacin da Hunter Biden ya sayi wata bindiga kirar revolver a wani shagon sayar da bindiga dake Delaware.
Bayan kimanin sa’o’i uku ana tattaunawa, alkalan kotun sun samu Hunter da laifin yin karya game da amfani da muggan kwayoyi da kuma mallakar bindiga.
Wannan hukuncin ya kasance wani lokaci mai tarihi domin shine karo na farko da aka samu dan gidan shugaban kasa da laifi, a lokacin mulkin mahaifinsa, duk da cewa laifin Hunter Biden ya faru ne kafin Joe Biden ya zama shugaban kasa.
Hunter Biden na fuskantar daurin shekaru 25 a gidan yari da kuma tarar dala 750,000 a lokacin yanke hukunci, duk da cewa a matsayinsa na mai laifin farko, akwai yuwuwar yanke masa hukunci kadan. Ana sa ran yanke hukunci a cikin kwanaki 120.
Masu gabatar da kara, karkashin jagorancin lauya na musamman David Weiss, y ace, ayyukan Hunter Biden, sun saba wa dokokin da ke nufin hana masu shan muggan kwayoyi tare da mallakar bindigogi.
Hukuncin ya kawo karshen wani babi na binciken da ma’aikatar shari’a ta yi kan Hunter Biden, wanda aka fara a shekarar 2018. Ana sa ran zai sake fuskantar wata shari’a a watan Satumba saboda laifukan haraji na tarayya.
Dukkan shari’o’in biyu David Weiss ne, wanda shugaba Trump ya nada a baya, wanda tawagarsa ta musanta wani dalili na siyasa da ke tattare da tuhumar.
Duk da hargitsin doka, Shugaba Biden da Fadar White House sun yi watsi da afuwa ga Hunter Biden.