fidelitybank

Kotu ta samu babban jami’in Soja da sace kuɗaɗe

Date:

Wata kotun soja ta musamman a Najeriya, ta sanya ranar 10 ga watan Oktoba don yanke hukunci kan shari’ar da ta yi wa wani babban hafsan soja mai mukamin manjo janar, bisa tuhume-tuhumen sata da yin jabun takardu da almubazzaranci da kuma shirya maƙarƙashiya.

Manjo janar Umaru Muhammed, tsohon Manajan Darakta na kamfanin kula da kadarorin rundunar sojojin kasa ta Najeriya wato Nigerian Army Properties Limited ya gurfana a gaban kotun ne a kan tuhume-tuhume guda 18.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito shugaban kotun, Manjo Janar James Myam, na cewa wanda ake tuhumar a ranar Laraba, ya ƙi amsa laifi a kan kararrakin da aka gabatar a kansa, inda ya gabatar da shaida biyu a kotu.

Ya ce a daya bangaren kuma mai kara wato rundunar sojin kasa ta Najeriya ta gabatar da shaida 24 a tsawon shari’ar da aka yi.

Janar James Myam ya ce tuhuma ta ɗaya an shigar da ita ne a ƙarƙashin sashe na 383, karamin sashe na kundin dokar manyan laifuka na Najeriya.

Myam ya kara da cewa, an kuma gabatar da tuhumar ne bisa sashe na 114 na dokar Sojoji Cap A20 2004.

Kotun ta ce ta samu hafsan da ake kara da laifin satar dalar Amurka miliyan 1.04 tsakanin 7 ga watan Mayun 2019, zuwa 24 ga watan Yunin 2021, lokacin da yake aiki a matsayin manajan daraktan kamfanin NAPL.

Babban alkalin kotun ya kuma ce an samu wanda ake tuhuma – da laifin bai wa wani, Manjo Usman da wani mutum wanda a halin yanzu ake neman su – umarni su dinga karbar kudi da dalar Amurka daga hannun masu jiragen ƙasa.

Sai dai Janar Myam ya ce ba a samu Janar Umaru Muhammed da laifi ba a tuhuma ta 7, wadda ta kunshi laifin hada baki don yin jabun takardu tare da wani Yusuf Abdulahi.

Haka zalika shugaban kotun ya ce an kuma samu Janar Umaru Mohammed da laifin yin jabun takardu mai alaka da tuhuma ta 8 da ta 9 a kan satar dala 430,000.

Kotun ta kuma samu wanda aka yi karar da laifin shirya makarkashiya don yin jabun takardu da sayar da kadarar kamfanin rundunar sojojin kasa a kan naira miliyan 200.

Sannan ta same shi da laifin daukar kudi naira miliyan 74 cikin wata hanya ta rashin gaskiya daga asusun kamfanin a ranar 22 ga watan Agustan 2019.

Game da tuhuma ta 14 da 15 da 16 da kuma ta 18, wadanda suka danganci babban laifin yin sama da fadi, kotun ta ce wanda aka yi zargin bai iya yin bayani a kan dukiyar da ta kai naira biliyan 2 da rabi mallakar kamfanin soja ba. In ji BBC.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp