fidelitybank

Kotu ta sami Okupe da laifin karbar Naira miliyan 200

Date:

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu na babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin ta samu babban mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara (SSA), Dr Doyin Okupe da laifin karbar kudi sama da naira miliyan 200 daga hannun tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki. .

Mai shari’a Ojukwu a hukuncin da ta yanke ya ce matakin da Okupe, wanda shi ne wanda ake kara na farko a karar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta EFCC ta shigar ya saba wa dokar satar kudi.

Yayin da yake bayyana cewa dokar ta tanadi cewa babu wani mutum ko wata kungiya da za ta karbi kudin da ya haura Naira miliyan 5 da miliyan 10 ba tare da wucewa ta wata cibiyar hada-hadar kudi ba, alkalin ya ce “babu wata shaida da ke nuna cewa kudaden sun bi ta wata cibiyar kudi”.

A cewar mai shari’a Ojukwu, hukumar NSA ba cibiyar hada-hadar kudi ba ce, inda ya kara da cewa ko da a ce shugaban kasa ne ya ba da izini bai ce dole a biya kudin a cikin tsabar kudi ba, wanda ya saba wa halasta kudaden haram.

Don haka kotun ta ce, “Na samu wanda ake kara na farko, Doyin Okupe da laifi a kirga 34, 35, 36…… 59.”

vangurd 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp