Wata Kotun Majistare da ke Kaduna a ranar Talatar, ta bayar da umarnin a yi wa wani, Ezekiel Francis, mai shekaru 28, bulala 10 bayan ya saci Naira 20,000.
Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya bayar da umarnin ne bayan Francis ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi tare da rokon kotun da ta yi masa sassauci.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya ce daga bayanan kotun, an yankewa wanda ake tuhuma hukuncin daurin shekara daya a gidan yari bisa laifin sata a shekarar 2022.
Emmanuel ya kuma yankewa Francis hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ba tare da zabin tara kudi ba, sannan ya gargade shi da ya daina aikata laifuka kuma ya kasance mai halin kirki daga yanzu.
Ya jaddada cewa kotu ba za ta sake yi masa sassauci ba.
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a unguwar Karji da ke Kaduna a ranar 5 ga watan Janairu.
A cewar Leo, wanda ake kara da daya daga cikinsu, sun sace N20,000 daga gidan wani Caleb Vincent.
Ya ce an kama wanda ake tuhuma ne yayin da wanda ake tuhuma ya tsere.
Leo ya lura cewa laifin ya ci karo da sashe na 217 na kundin laifuffuka na jihar Kaduna, 2017.


