Wata babbar kotu a jihar Kano, ta gurfanar da wani Ibrahim Khalil Danshagamu, mai fafutukar yada labaran yanar gizo, bisa samunsa da laifin bata sunan tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya.
Mai shari’a Halima A.B ta jagoranta ta tasa keyar sa. Danshagamu wanda ake kara dai an gurfanar da shi a gaban Kotu, bisa zarginsa da yada wani faifan bidiyo a shafukansa na sada zumunta, inda ya yi ikirarin cewa, Buratai ya gina gidajen mai sama da 60 a Kano daga cikin kudin sayen makamai.
Tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin (Buratai), ya bukaci ‘yan sanda da su kamo wanda ake tuhuma don tabbatar da ikirarin.
Danshagamu wanda ake tuhuma ya musanta tuhumar da ake yi masa bayan da ‘yan sanda suka kama shi.
Lauyan wanda ake kara, Barista S.A Abdullahi, ya roki kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa, amma alkalin kotun ya ki amincewa da hakan, saboda laifin da ake tuhumar ya saba wa sashi na 371 da 115, saboda laifin da ake tuhumar zai kai ga daurin shekaru uku a gidan yari.
Don haka alkalin ya ba da umarnin a aika wanda ake kara zuwa ga likitan hauka na jihar don tantance ko yana cikin ma’anarsa a lokacin da ya raba faifan bidiyon.
Lauyan wanda ya shigar da karar Barista Hussaini Makari, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman kotun, ya bayyana cewa, wanda yake karewa ya kuma jefa kalubalen cewa, a shirye yake ya janye karar da ake tuhumar wanda ake kara idan har wani dan jihar Kano zai iya nuna wani abu.