Babbar Kotun Jihar Nasarawa da ke Akwanga ta yanke wa Gambo Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Hassan Ahmed.
Da yake jagorantar shari’ar, Mai shari’a Mustapha Ramat ya samu Adamu da laifin kashe Ahmed ta hanyar girbe sassan jikin sa, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci da rashin mutuntaka.
An yanke hukuncin ne a ranar Talata a Akwanga.
Babban Lauyan Jihar Nasarawa kuma Kwamishinan Shari’a, Dakta Labaran Shu’aibu Magaji, ya yaba da hukuncin a matsayin “Nasara ce ga al’ummar Jihar Nasarawa” da kuma gargadi mai tsauri na dakile ayyukan aikata laifuka a nan gaba.