Rigimar jamâiyyar APC a jihar Anambra ta rikide, bayan da kotu ta tsoma bakin ta, rushe zaben shugabannin da aka shirya a watan da ya gabata.
Jaridar Daily Trust ta ce, wata babban kotu da ke zama a Awka, jihar Anambra ta rushe zaben APC.
Tsofaffin shugabannin APC 17 a karkashin jagorancin Lawrence Emegini, suka kai jamâiyyarsu kotu, su na korafin cewa, har zuwa yanzu waâadinsu bai kare ba.
A wata kara mai lamba 2022 A/3/2022, tsofaffin shugabannin rikon kwarya na mazabu da kananan hukumomi sun kalubalanci ingancin zaben da aka gudanar.
A ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu 2022, Alkalin babban kotun da ke zama a garin Awka, Ike Ogu, ya zartar da hukuncin, da ya baiwa jamâiyyar APC rashin gaskiya.


