Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jalingo a ranar Talata ta soke zaben fidda gwani na gwamnan jihar Taraba, da ya samar da Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress a zaben 2023.
David Kente, wanda ya fusata ya kai jam’iyyar da dan takararta kotu kan amincewa da Bwacha a matsayin dan takarar jam’iyyar.
A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun mai shari’a Simon Amobeda, ya bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda gwani a cikin kwanaki 14.
Kotun ta kuma umarci Bwacha da ya daina bayyana kansa a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar APC.