Kotun ƙoli ta jingine shari’ar kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour na ƙasa.
A wata shari’a da alƙalan kotun guda biyar suka yanke, kotun ƙolin ta ce kotun ɗaukaka ƙara ba ta da hurumin tabbatar tabbatar da sahihancin shugabancin jam’iyya.
Kotun ta ce batun shugabanci, lamari ne da ya shafi jam’iyya, kuma kotu ba ta da hurumin yin katsalandan.