fidelitybank

Kotu ta nemi El-Rufai ya biya diyyar miliyan 900 kan tsare wasu Dattawa

Date:

Wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta yanke hukunci inda ta nemi tsohon gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai, da wasu mutum biyar su biya diyyar naira miliyan 900 a matsayin diyyar tsare wasu dattawan Adara da ke ƙaramar hukuma Kajuru a jihar ba bisa ƙa’ida ba a shekarar 2019 a ƙaramar hukumar Kajuru.

Gidan talbijin na Channels wanda ya rawaito labarin ya ce mai shari’a Hauwa’u Buhari ce ta yanke hukuncin a kan ƙarar da Awemi Dio Maisamari da wasu dattawan Adara takwas suka shigar, inda kotu ta tabbatar da cewa an tsare su ne bisa zargin hannu a kisan sarkin gargajiyarsu, Raphael Maiwada Galadima, ba tare da wani dalilin doka ba.

Kotu ta ce El-Rufai ya ci gaba da matsa lamba a kan a kama su, kuma ya aikata hakan ne ba a matsayinsa na gwamna ba.

Kotu ta yi watsi da korafe-korafen da waɗanda ake ƙara suka gabatar.

Lauyar da ta wakilci masu ƙarar, Gloria Ballason, ta bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara a yaƙi da cin zarafin da gwamnoni da shugabanni ke yi da amfani da karfi da ikon da ke hannunsu.

Dattawan takwas, ciki har da tsohon kwamishina na ƴan sanda mai ritaya, an kama su ne a wani taron al’umma da El-Rufai ya shirya a shekarar 2019, bayan sace da kashe sarkinsu.

@nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp