Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da wata babbar kotun tarayya a birnin ta yanke, inda ta tisge Godswill Akpabio a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso yamma a Majalisar Dattijai.
Hukuncin kotun wanda alkalai uku suka yanke da mai shari”a Danlami Senchi ya karanta a ranar Litinin ya ce Akpabio ya gaza gabatar da shaida a cikin lokacin da doka ta tanada.
Alkalan sun kuma ce, kasancewar Akpabio, dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, ba zai iya shiga sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 27 a watan Mayu ba wanda aka yi a gaban jami’an hukumar zabe mai zaman kanta inda aka gabatar da Udom Ekpoudom a matsayin dan takarar jam’iyyar.
A hukuncin da wata babbar kotun tarraya da ke Abuja ta yanke a ranar 22 ga watan Satumba ta nemi hukumar ta INEC ta mayar da Sanata Akpabio a matsayin dan takarar jam’iyyar ta APC, a matsayin dan takarar da ta tsayar a zaben fid-da-gwani karo na biyu da aka yi a ranar 9 ga watan Yuni.