fidelitybank

Kotu ta kuma daure tsohuwar shugabar Myanmar Suu Kyi a kan magudin zabe

Date:

Kotun sojin Myanmar ta yankewa tsohuwar shugabar kasar Aung San Suu Kyi, karin daurin shekara uku a gidan kaso kan laifin magudin zabe, kamar yadda lauyanta ya shaidawa BBC.

Ms Suu Kyi dai na zaman kason daurin shekara 20 kan laifuka 11 da ake zarginta da shi, har ma da wasu karin laifukan da ba a kai yin shari’arsu ba.

Ta musanta dukkan zarge-zargen da akai mata, a shari’ar da masu rajin kare hakkin dan adam sukai allawadai da zargin gwamnatin soji da yi ma ta bita da kullin siyasa.

Lauyan tsohuwar shugabar, ya ce cikin sabon hukuncin da aka yanke mata har da aiki mai tsananin gaske.

Suu Kyi mai shekara 76 da ta taba daukar lambar yabo ta Nobel, ta shafe yawancin rayuwarta karkashin daurin talala a babban birnin kasar Nay Pyi Taw.

Sojojin Myanmar din sun hana mutane da ‘yan jarida damar shiga kotun a lokacin da ake yanke hukuncin, an kuma hana hatta lauyoyin ta ba a ba su damar magana da ‘yan jarida ba.

Ms Suu Kyi da yawancin mambobin jam’iyyar ta na daga cikin sama da mutum 15,000 da gwamnatin sojin da ta yi juyin mulki a Myanmar ta daure tun bayan karbe kasar.

Har yanzu mutum 12,000 na gidan kaso daban-daban da ke Burma.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp