Wata kotu a Myanmar ta yanke wa hamɓararriyar shugabar kasar, Aung San Suu Kyi, hukuncin ƙarin shekara shida a gidan kaso, bayan samunta da laifukan cin hanci da rashawa.
Wakilin BBC ya ce laifukan da ake tuhumar Aung-San Suu Kyi da su sun haɗa da karkatar da kuɗin tallafin da aka bayar domin bunƙasa fannin lafiyar ‘yan Burma, wanda aka ba da a asusun kungiyar da ta sanyawa sunan mahaifiyarta, inda ta karkatar da kudaden asusunta da gina gidan alfarma.
An yanke wannan hukunci ne ba tare da an bai wa mutane damar shiga kotun ba, ciki har ‘yan jarida.
Kuma Ms Suu Kyi ta sha musanta aikata ba daidai ba kan tuhume-tuhumen da akai mata.
Tuni dai ta ke zaman shekara 11 da aka yanke mata kan wani laifin na almundahana, a shari’ar farko tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun shekarar da ta gabata, nan ma ta musanta zargin.


