Rikicin shugabanci da ya dabaibaye hukumar kwallon kafa ta jihar Taraba (FA), ya dauki sabon salo.
Wannan na zuwa ne yayin da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jalingo, babban birnin jihar, ta kori shugaban da ke kan karagar mulki, Timothy Heman.
Alkalin kotun, Mai shari’a Simone Amobeda ya bayar da umarnin a gaggauta rantsar da wanda ya shigar da kara, Sanusi Mahmoud a matsayin shugaban kungiyar a jihar.
Rikicin, wanda aka shafe shekaru uku ana yi, ya yi illa ga harkar kwallon kafa a Jihar.
Alkalin ya gargadi shugaban mai ci da cewa cikin gaggawa ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban hukumar FA ta jihar.
Kotun ta kuma umarci kungiyar a matakin kasa da ta daina hulda da shugaban da ke kan karagar mulki.
Da yake jin dadin sakamakon hukuncin, lauyan Mahmoud Isa Buba, ya bukaci wadanda suka yi korafin su hada kai da Mahmoud domin ciyar da kwallon kafa gaba a Taraba.