Kotun daukaka kara da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar na a dage shari’ar a wata bukatar da ta bukaci a dakatar da aiwatar da hukuncin da ya soke tuhumar ta’addancin da ake yi wa dan fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.
A maimakon haka dai kotun ta baiwa gwamnatin tarayya har zuwa tsakar yau da ta mika bukatar ta ko kuma ta manta da ita.
Lauyan gwamnatin tarayya, Mista David Kaswe, a zaman na yau, ya koka da cewa lauyan Kanu, Cif Mike Ozekhome SAN, ya ba shi takardar amsa tun ranar Juma’ar da ta gabata.
Sai dai Kaswe ya yi ikirarin cewa an ba shi jerin sunayen karin hukuma daya a safiyar yau kuma yana bukatar a dage zaman don mayar da martani.
Sai dai Ozekhome, ya ki amincewa da bukatar ne bisa hujjar cewa karin hukuma daya ce kawai, kuma bai kamata Gwamnatin Tarayya ba ta da uzuri na neman a dage zaman saboda hukuma daya kacal.
Ozekhome ya yi ikirarin cewa tun ranar 13 ga watan Oktoba da kotun daukaka kara ta bayar da umarnin a saki Kanu, gwamnatin tarayya ba ta bi umarnin ba.
Ya tunatar da kotun cewa ana tauye hakkin ‘yancin kai na wanda yake wakilta, don haka ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar a dage shari’a.
A wani takaitaccen hukunci da shugaban mai shari’a Haruna Tsanami ya yanke, ya amince da cewa karar na da nasaba da muhimman hakkokin bil’adama kuma ya cancanci a dauki matakin gaggawa.
Daga bisani mai shari’a Tsanami ya baiwa gwamnatin tarayya har zuwa tsakar rana da ta mika bukatarta na dakatar da zartar da hukuncin da kuma mayar da martani ga sabuwar hukumar da kungiyar lauyoyin Kanu ta kawo.


