Kotun ƙoli a jihar Colorado ta Amurka ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump bai cancanci tsayawa takara ba a jihar kuma ba zai iya fitowa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar Republican a shekara mai zuwa ba.
Kotun ta ce saboda abin da tsohon shugaban ya yi a ranar 6 ga Janairun 2021 – ranar da aka kai hari kan ginin majalisa – Capitol hill – da aka yi wa kallon yunƙurin tayar da zaune tsaye.
Ofishin yaƙin neman zaben Trump ya kira hukuncin kotun a matsayin abin da ya saɓawa dimokradiyya, sannan kuma ya ce zai ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙolin tarayya.
Za a jingine hukuncin har sai kotun tarayya ta yanke nata, to amma duk da haka jami’an zaɓe a Colorado sun ce akwai buƙatar a yi abin da ya dace kafin nan da 5 ga watan Janairun 2024.
Hukuncin bai hana Trump tsayawa takara ba a sauran jihohin Amurka.


