Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta haramtawa hukumar kula da kafofin yada labarai na NBC cin tarar tasoshin talabijin a faÉ—in Najeriya.
Alkali James Omotosho, a wani hukunci da ya yanke ranar Laraba ya ce hukumar NBC ba ta da karfin ikon hukunta kafofin watsa labarai kai-tsaye.
Alkali Omotosho ya kuma dakatar da tarar dala 1,084 da NBC ta ci wasu kafofin watsa labarai 45 a faÉ—in kasar kan karya dokokin aiki daga watan Maris.
Ya ce kotu ba za ta zura ido NBC na cin tara ba tare da bin ka’idojin doka ba.
Kungiyar manyan editoci ta Najeriya ta yi murna da wannan hukunci na kotu, wanda take cewa zai kwato ‘yancin aikin jarida.