Kotu a birnin Osaka na Japan ta tabbatar da haramcin auren jinsi a kasar, wanda tace matakin bai saba wa kundin tsarin mulki ba.
Hukuncin kotun bai yi wa yan luwadi da ke son auren juna dadi ba, bayan da a baya kotu a birnin Sapporo tace hana su auren ya saba wa kundin tsarin mulki.
Dama kundin tsarin mulkin Japan ya shimfida cewa aure na faruwa ne kawai a tsakanin jinsin mace da na namiji.
Ita kadai ce kasa daya tilo a cikin jerin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki na G7 da bata yadda da auren jinsi ba. A cewar BBC.
Shine karo na biyu da aka taba shigar da kara a Japan kan neman bada damar auren jinsi a kasar, amma kuma hakan bata samu ba.