A ranar Talatar da ta gabata ne aka hana ‘yan jarida da ke sauraron shari’ar DCP Abba Kyari da aka dakatar da sauran su shiga harabar kotun ta 10 na babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Mai shari’a Emeka Nwite ya ba da wannan umarni ne biyo bayan bukatar da lauyan hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Mista Sunday Joseph ya gabatar.
Joseph, wanda darakta ne na sashin shari’a da kara na NDLEA, a baya ya nemi a ba da kariya ga shaidar wanda ya bayar da shaida a shari’ar.
Lauyan ya roki kotun da kada ta bari sauran Lauyoyi, masu ziyara, masu kara da ‘yan jarida su shiga cikin kotun yayin zaman na ranar Talata.
Daga nan sai mai shari’a Nwite ya yi watsi da batun domin bai wa wadanda ba sa cikin jam’iyya damar shigar da kara a kan ‘yan sandan da aka dakatar da su fice daga cikin kotun.