fidelitybank

Kotu ta hana gwamnan Sokoto tsige Hakimai

Date:

Babbar kotu a jihar Sokoto ta dakatar da gwamnan jihar, Ahmed Aliyu daga tumbuke rawanin mutane biyu daga cikin hakimai 15 da gwamnatinsa ta tsige.

Hakiman Tambuwal da Kebbe, Alhaji Buhari Tambual da Alhaji Abubakar Kassim, wadanda ke cikin hakiman da gwamnatin jihar ta tube ne suka shigar da karar.

Gwamnatin ta dauki mataki a kan su ne bisa zargin hannu a matsalar tsaro da kuma kin yin biyayya.

Alkalin kotun, mai shari’a Kabiru Ibrahim Ahmed, ya bai wa gwamnan da alkalin alkalan jihar da fadar sarkin musulmi da su soke tubewar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da hakiman suka shigar gabansa ta hannun lauyansu Farfesa Ibrahim Abdullahi mai mukamin SAN.

Mai shari’a Ahmed ya umarci wadanda ake kara da wakilansu da su tsaya kan matsayin da ake game da batun tsige hakiman a jihar Sokoto musamman hakiman Kebbe da Tambuwal har sai lokacin da aka kammala sauraron karar da suka shigar gaban kotu.

Tuni dai korar hakimai 15 da kudirin da ke neman yin garambawul ga dokar kananan hukumomi a Sokoto, suka janyo cece-kuce a fadin kasar nan, inda mataimakin shugaban kasa, Kassim Shetiima ya nemi gwamnatin jihar ta mutunta kujerar sarkin musulmi.

sunnnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp