fidelitybank

Kotu ta hana CBN ya daina tura wa Gwamnan Rivers kason kuɗin su na wata-wata

Date:

Mai shari’a Joyce Obehi Abdulmalik na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya umarci babban bankin CBN da ya dakata da bai wa jihar Rivers kason ta daga asusun gwamnatin tarayya na wata-wata.

Mai shari’a Joyce Obehi Abdulmalik ya ce, kuɗaɗen kason da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara yake karɓa daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa yanzu ya saɓa doka, kuma dole a dakatar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Alƙalin ya ce, gabatar da kasafin kuɗin da gwamna Fubara ya yi a gaban ƴan majalisar jihar guda huɗu kacal ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Wannan ya sa alƙalin ya buƙaci babban bankin CBN da akanta-janar na ƙasa da bankin Zenith da bankin Access da su tabbatar Fubara bai ci gaba da amfani da kason jihar na wata-wata ba.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...
X whatsapp