Kotun da ke sauraren ƙarar zaben shugaban kasa da aka yi, ta hade kararraki guda uku da ‘yan hamayya suka shigar gabanta a kan sakamakon zaben wanda hukumar zabe INEC ta bayyana Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Wadanda suka shigar da kararrakin su ne dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da jam’iyyarsa, sai Peter Obi tare da jam’iyyarsa ta Labour, sai kuma jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).
A rahoton da kotun mai alkalai biyar ta fitar wanda jagoranta Mai shari’a Haruna Tsammani ya karanta yau Talata, ta kotun ta umarci fara sauran korafin su Peter obi da jam’iyyarsa ta Labour a ranar 30 ga watan Mayun nan.
Kotun ta umarci masu karar da su gabatar da korafe-korafensu a cikin mako uku wanda cikin lokacin za ta kirawo masu gabatar da shedar da aka ware guda 50, daga ranar 30 ga watan na Mayu a lokacin da za masu korafin za su fara kiran masu sheda a kuma kammala a ranar 23 ga watan Yuni.
Kotun ta ce za a kammala shari’ar a ranar 5 ga watan Agusta a lokacin da lauyoyn masu karar za su gabatar da jawabansu na karshe a rubuce, daga nan kuma kotun za ta ware ranar da za ta bayyana hukuncinta