Wata babbar kotun jihar Kano ta yai gargaɗi kwamishinan ‘yan sandan jihar da Sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya da darektan jam’ian tsaro na DSS da hafsan hafsoshin Najeriya da kuma sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da su guji cusgunawa Sarkin kano Muhammadu Sanusi II.
Takardar kotun mai ɗauke da sa-hannun rijistarar kotun, Umar Mustapha, ta yi ƙarin bayani kan abin da take nufi da cusgunawa da ta haɗa da ƙoƙarin fitar da Sarki Sanusi daga gidan Rumfa ko ƙwace tagwayen masu ko kuma duk wani abun da zai janyo wulaƙanci ga Sarkin.