Wata kotun majistare da ke zamanta a Kano, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 37, Jamilu Ahmed, a gidan gyaran hali, bisa zarginsa da dukan kaninsa, Alhassan, mai shekaru 30 har lahira.
Lauyan masu gabatar da kara, Aminu Dandago, ya shaida wa kotun cewa Ahmed ya aikata laifin ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2022 a Chediyar Kuda Quarters Kano.
Dandago ya yi zargin cewa a daidai wannan rana da misalin karfe 10 na dare Ahmed ya yi ta bugun kanin nasa akai-akai a cikin rashin fahimta.
Ya ce marigayin ya samu raunuka a ciki kuma an kai shi Asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano inda aka tabbatar da rasuwarsa a lokacin da yake karbar kulawa.
Laifin, in ji mai gabatar da kara, ya saba wa tanadin sashe na 221 na kundin laifuffuka.
Alkalin kotun Farouk Ibrahim-Umar, bai karbi rokon Ahmed ba.
Ibrahim-Umar ya umurci ‘yan sanda da su mayar da fayil din karar ga daraktan kararrakin jama’a na jihar Kano domin samun shawarar lauya.
Ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 8 ga watan Satumba